Kebbi: Sabuwar doka masu sace mutane zasu fuskanci kisa, fyade kuma daurin rai da rai


Gwamna Abubakar Atiku Bàgudu ya rattaba hannu a dokar da ta tabbatar da hukuncin kisa ga masu sace mutane da kuma dàurin rai da rai ga masu aikata fyade a jihar Kebbi.

Kwamishinan shari'a kuma Attoni janar a ma'aikatar shari'a na jihar Kebbi Hajiya Ramatu Gulma ta sanar wa manema labarai haka a garin Birnin kebbi ranar Alhamis.

Sabuwar dokar ta Penal Code 202 ta yi tanadin hukuncin kisa ga masu garkuwa/sace mutane karkashin sashe na 247 na dokar wadda ta tanadi hukuncin dàurin rai da rai karkashin sashe na 259 sub section (1) ga masu aikata fyade a fadin jihar Kebbi.

DAGA ISYAKU.OM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN