An sami bayyanar Annabi bakar fata bayan ikirari, duba abin da ya faru da shi


Jaridar yanar gizo ta legit ta wallafa cewa rundunar yan sanda a jihar Anambra ta kama wani fasto da ke kiran kansa Annabi Onyebuchi Okocha da aka fi sani da 'Onyeze Jesus' kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Onyeze Jesus a cikin wani sakon da ya wallafa a faifan bidiyo ya yi ikirarin cewa zai tada gawarwakin mutane bakwai da ke ajiye a dakin ajiye gawarwarki na asbiti wato 'mortuary'.

'Yan sanda sun kama wani mai iƙirarin 'Annabta' da ya ce zai tayar da matattu

Fitaccen mai wa'azin shine wanda ya kafa cocin Children of Light Anointing Ministries, Nkpor, a karamar hukumar Idemili North a jihar.

An kama shi ne a ranar Laraba 27 ga watan Janairun shekarar 2021.

Gwamnatin jihar ta bakin kwamishinan watsa labarai da wayar da kan al'umma na jihar, MR C. Don Adinuba, a ranar Juma'a, 25 ga watan Janarun 2021 ta gargade shi kan ayyukan da ya ke yi da gwamnatin ta ce 'laifi ne da rashin tarbiyya da sunan addini.

Kazalika, Ma'aikatan Lafiya na Jihar, a sanarwar da ta fitar a ranar Laraba ta gargadi asibitoci a jihar da masu ajiye gawarwaki kada su sake su bari mutumin ya shiga wurin da suke ajiye gawarwaki da sunan zai tada matattu da siddabaru.

Mutane da dama sun bayyana damuwarsu a kafafen sada zumunta kan bidiyon da Onyeze Jesus ya fitar na gardawa ba tare da kaya a jikinsu ba a cikin rafi yana watsa musu kudade da sunan wai za su yi arziki.

Kakakin yan sandan jihar, CSP Haruna Mohammed ya tabbatar da kama shi inda ya ce nan bada dadewa ba za a gurfanar da shi a kotu.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN