Abin tausayi, duba yadda Buratai ya mika wa Attahiru mulki


Kimanin sa'ao'i 24 bayan sanarwa, an yi taron mika mulki daga hannun wanda ya sauka daga karagar zuwa sabon da shugaban kasa ya nada, a yau Alhamis, 28 ga watan Junairu, 2021.

A wannan taro mai kayatarwa da aka gudanar a farfajiyar taron hedkwatar sojin kasa dake birnin tarayya Abuja, Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai, ya mika tutan fara aiki ga sabon shugaban hafsan Sojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru.

Buratai ya mika mulki ga sabon shugaban hafsan sojin kasa, Ibrahim Attahiru (Hotuna)


Buratai ya mika mulki ga sabon shugaban hafsan sojin kasa, Ibrahim Attahiru (Hotuna)

Buratai ya mika mulki ga sabon shugaban hafsan sojin kasa, Ibrahim Attahiru (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami dukkan hafsoshin tsaron Najeriya a ranar Talata, 26 ga watan Junairu, 2021, kuma ya nada sabbi ba tare da bata lokaci ba.

Mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina, ya bayyana haka a shafinsa na Tuwita.

A cewar Adesina, Buhari ya nada Manjo Janar Leo Irabor a matsayin shugaban hafsoshin tsaro; Manjo Janar Ibrahim Attahiru matsayin shugaban Sojin kasa; RA AZ Gambo matsayin shugaban sojin ruwa, da kuma AVM IO Amao matsayin shugaban mayakan sama.

A bangare guda, sakamakon sallaman Laftanan Janar Tukur Buratai matsayin shugaban hafsoshin Sojin Najeriya ranar Talata, ya zama babban hafsa mafi dadewa kan kujerar mulki a tarihin Najeriya.

Daily Trust ta bayyana cewa Janar Buratai dan asalin jihar Borno ya yi watanni 66 matsayin shugaban Sojojin kasan Najeriya.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN