Duba wani abin alhairi da kungiyar Makafi ta kasa reshen jihar Jigawa ta yi


Kungiyar Makaffi ta kasa reshen Jihar Jigawa wato National Association of the Blind (NAB) ta gudanar da taron addu'o'in Neman  zaman lafiya na shiyyar Jigawa Arewa maso yamma a garin Gumel, a nasa jawabin Uban Kungiyar Malam Musa Usaini Matoya yace sun gudanar da wannan taro ne domin yin addu'o'i akan halin rashin tsaro da ke faruwa a kasar nan da kuma kara yin addu'o'i akan cikar maimartaba sarkin Gumel shekaru Arba'in akan karagar mulkin Masarautar Gumel,daga karshe ya mika sakon godiya ga fadar maimartaba sarkin Gumel bisa tallafa musu da gudunmuwa domin gabatar da wannan taro.


A nasa jawabin Dayayi Da Manema Labarai Sakataren Kungiyar reshen Jihar Jigawa Malam Usaini Haladu Fulata ya Kara yin godiya ga fadar maimartaba sarkin Gumel da kuma Sakataren masarutar Gumel Alhaji Murtala Aliyu Muhammad da kuma maigirma Sa'in Gumel bisa ga gagarumar gudunmuwa da suke baiwa wannan kungiya tasu,daga karshe Yayi kira ga gwamnatin Jihar Jigawa da ta samar musu makarantar firamare ta yara makaffi a shiyyar Jigawa maso Arewa da kuma Jigawa maso Gabas kamar yadda aka Samar da irin ta a shiyyar Jigawa ta tsakiya.

Taron ya sami halartar manyan baki daga waje da cikin Jihar Jigawa, daga cikin manyan baki akwai Malam Basiru Daura Wanda yazo daga Jihar Katsina da kuma Shugaban kungiyar reshen Jihar Jigawa wato Malam Abdullahi Haruna Hadejia. Daka Alhaji Sani Sani Maigatari


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN