Duba abinda Kotu ta yi wa matashi da ya yi wa tsohuwa mai shekara 50 fyade

A jiya ne wata kotun majistare da ke garin Ado Ekiti ta bada umarni a tsare mai shekara 29 a Duniya a gidan kaso da ke babban birnin na jihar Ekiti rahotun jaridar legit

Jaridar Punch ta rahoto cewa ana zargin wannan mutumi mai suna Olaleye Jimoh, da laifin yin lalata da wata Baiwar Allah mai shekaru 50 da haihuwa.

Jami’in ‘yan sanda, Oriyomi Akinwale, ya shaida wa kotu a ranar Alhamis, 28 ga watan Junairu, 2021, cewa ana zargin Mista Olaleye Jimoh da laifin fyade.

Akinwale ya ce an kama matashin ne a ranar 24 ga watan Junairu, 2021, a shiyyar Odo-Owa Ekiti, garin Ikole Ekiti, ana zargin ya aikata laifin ne kafin ranar.

A cewar jami’in tsaron; “Za a hukunta duk wanda ya aikata irin wannan laifi a karkashin sashe na 358 na dokokin laifuffukan jihar Ekiti na shekarar 2012.”

Rahoton ya bayyana cewa Akinwale ya roki kotu ta ba shi damar ya dauki takardar karar ya kai wa darektan tuhuma domin a dauki matakin da ya kamata.

Olaleye Jimoh ya bayyana a gaban kotu, yayin da ya samu wani lauya mai suna, Busuyi Ayorinde, ya tsaya domin ya ba shi kariya daga zargin da ake yi masa.

Alkali mai shari’a, Adefunmike Anoma ta saurari karar, a karshe ta ce a tsare wanda ake zargin.

A ranar 4 ga watan Maris, 2021, mai shari’a Adefunmike Anoma, za ta cigaba da zama domin ta karasa sauraron karar bayan an dakatar da zaman a ranar Alhamis.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN