Bidiyo: Wasu mutane sun kori Fulani tare da kone bukkokinsu a jihar EbonyiRahotanni daga jihar Ebonyi sun yi zargin cewa wasu mutane sun takura tare da rushe bukkakin Ruggan Fulani a wasu sassan jihar wanda fusatattun matasa ke gudanarwa.


Bayanai sun ce matasan na zargin Fulani da takura wa iyayensu, lamari da suka yi zargin cewa ya hana iyayensu gudanar da ayyukan gona.

Kalli bidiyo a kasa

Wani faifen bidiyo da ya bayyana a yanar gizo, ya nuna yadda wasu mutane ke rushewa tare da kone iya abin da ke konuwa a ruggar Fulani. Sun kuma kalubalanci Fulani cewa su kai kokensu wajen Gwamna Dave Umuahi na jihar Ebonyi.


Mutanen sun sha alwashin ganin cewa sun raka Fulani har inda suka fito domin tabbatar da cewa sun fice daga yankunansu har abada.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari