Hukumar lura da wutan lantarkin Najeriya NERC, ta karyata rahoton cewa ta kara farashin wutan lantarki na kashi 50 kan abinda kwastamomi ke biya yanzu a fadin tarayya.
NERC a shafinta na Tuwita ta bayyana cewa har yanzu bata bada umurnin kara farshin wuta ba kamar yadda kafafen yada labarai ke watsawa.
"Hukumar (NERC) ta samu labarin wallafe-wallafe da ake yadawa a kafafen yada labarai inda ake fadawa mutane cewa hukumar ta kara farashin wutan lantarki da 50%," hukumar tace.
"Hukumar na mai bayyana cewa babu wanda ya bada umurnin kara farashin wutan lantarki da 50% a umurnin da ta baiwa kamfanonin raba wutan lantarki a ranar 1 ga Junairu, 2021."
"Saboda haka, muna kira ga kamfanonin jarida su janye abubuwan da suka wallafa."
Source: Legit
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari