Asiri ya tonu: An kama Trump yana shirya magudi lokacin zabe


Trump ya nemi wani jami'in gwamnatin jihar Georgia ya 'nemo' kuri'un kayar da Biden

Bayanan bidiyo,

Donald Trump: "Ina buƙatar samo ƙuri'u 11,780"

An bayyana wata hira da aka naɗa da Shugaban Amurka Donald Trump yayi, wadda a ciki yake gaya wa wani babban jami'in zabe na jihar Georgia da ya "nemo" isassun kuri'un da za su sauya akalar sakamakon zaɓen shugaban kasa da aka yi cikin watan Nuwamba.

"Ina bukatar a nemo min kuri'u 11,780," inji Mista Trump cikin wani faifai da aka naɗa yana umartar Brad Raffensperger, sakataren gwamnatin Jihar Georgia, kuma ɗan jam'iyyar Republican ya aikata wannan babban laifin na maguɗin zaɓe.

An ji Mista Raffensperger na gaya wa Mista Trump cewa sakamakon jihar Georgia daidai ya ke.

Mista Joe Biden ne ya lashe zaɓen jihar Georgia da wasu jihohin, inda ya lashe zaben shugaban ƙasa da ƙuri'u 306, shi kuma Trump ya sami 232.Amma tun ranar zaɓen ta 3 ga Nuwamba, Mista Trump ya riƙa iƙirari cewa an yi gagarumin maguɗi a zaɓen ba tare da ya samar da wata hujja ba.

Kawo yanzu dai, dukkan jihohi 50 na Amurka sun fitar da sakamakon zabukansu a hukumance, kuma kotunan Amurka sun yi watsi da kararraki 60 da aka shigar na sauya sakamakon da ya ba Mista Biden nasara.

Ranar 6 ga watan Janairu majalisar kasa za ta tabbatar da sakamakon zaben a hukumance.

Mista Biden, wanda dan jam'iyyar Democrat ne, za a rantsar da shi ne ranar 20 ga watan nan na Janairu.

2px presentational grey line

Wai me Trump ya ce ne cikin hirar?

Cikin wani bangare da jaridar Washington Post ta fitar, ana iya jin shugaban na Amurka na roƙon jami'in, a wani lokacin kuma yana gargadin sakataren gwamnatin na Georgia.

Ya dai nanata cewa shi n ya lashe zaɓen na Georgia kuma ya gaya wa Mista Raffensperger cewa babu laifi ko ƙalilan idan "ka ce ka sake ƙidayar ƙuri'un".

Amma an ji Mista Raffensperger na mayar wa Mista Trump cewa: "Kalubalen da ka ke fda shi a nan shi ne alƙaluman da ka ke da su ba na daidai ne ba."

Can cikin tattaunawar, Msta Trump ya ce ana raɗe-raɗi cewa wasu na kekketa kuri'u, kuma suna ɗauke na'urorin zaɓe daga ƙaramar hukumar Fulton County ta jihar - ikirarin da Mista Raffensperber ya musanta.

Daga nan ne shugaban na Amurka ya fara yi wa jami'in kashedin daukar matakin shari'a kansa.

"Ka san abin da suka yi amma ka ki sanar da kowa. Wannan babban laifi ne. Bai kamata ka kyale haka ya faru ba. Wannan babbar kasada ce a gareka da kuma ga Ryan, lauyanka," inji Mista Trump.

Daga nan ne ya ce a nemo ma sa wasu ƙuri'u 11,780 - wadanda za su ba shi jumillar kuri'u 2,473,634 a jihar, wato ya doke Mista Biden - wanda ya sami kuri'u 2,473,633 da kuri'a daya ke nan.

Ya bukaci Mista Raffensperger da ya sake duba sakamakon zaben na jihar.

"Kana iya sake duba sakamakon, amma ka sake dubawa da wadanda ke neman samar da amsoshi, ba wadanda ba sa son samar da amsoshi ba," inji shi.

Sai Mista Raffensperger ya mayar ma sa da martani cewa: "Amma Shugaba, ka san kana da mutanen da ke mika bayanai, mu ma muna mutanen da ke mia mana bayanai, kuma daga nan ne bayanan ke kai wa ga kotuna, wadda ita ce ke da hurumin yanke hukunci. Dole ne mu tsaya kan alkaluman da muke da su. Mun tabbata alkalumanmu ma su kyau ne."

Ranar Lahadi sai Mista Trump ya wallafasako a Twitter cewa Mista Raffensperger ya ki mika bayanan magudin zaben da shugaban ya ke ikirarin an yi. "Bai san komai ba!", inji shugaban cikin sakon.

Mista Raffensbperger ya mayar wa shugaban martani a shafinsa na Twitter: "Cikin mutuntawa Shugaba Trump: Abin da ka ke faɗi ba gaskiya ce ba. Gaskiya za ta bayyana."

Kauce wa Twitter, 1

Karshen labarin da aka sa a Twitter, 1

1px transparent line

Kawo yanzu dai Fadar White House ba ta ce uffan ba kan wannan faifan da aka fitar.

Amma babban dan majalisar tarayya daga jam'iyyar Democrat Adam Schiff ya ce: "An kware zanin yaudara da Trump kerufa da shi. An sake kama shi hannu dumu-dumu. A faifai."

Shi kuma Adam Kinzinger, wani dan jam'iyyar Republican mai matsakaicin ra'ayi, shi ma ya fitar da sakon Twitter: "Wannan gagarumin abin kunya ne. Ga dukkan 'yan majalisa da ke tunanin kalubalantar sakamakon wannan zaben, ina cewa babu wata hujja da za ku iya dogara da ita - musamman bayan da aka yi wannan tonon sililin - ba tare da kun zalunci kanku ba"

Source: BBCHausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN