2023: Babu karba - karba a tsarin APC Inji Sanata Shekarau, duba abin da ya ce


Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce babu wani tsarin karɓa-karɓa a kundin tsarin gudanarwa na jami'iyyar APC.

Sanatan, ya yi kira da masu kaɗa ƙuri'a da su mayar da hankalinsu kan ɗan takarar da ya cancanta maimakon tsarin shiyya-shiyya, kamar yadda Premium Times ta rawaito.

A cewar Malam Shekarau, ingancin ɗan takara shine ya kamata ya zama muhimmin abin dubawa a zaɓe mai zuwa, ya ƙara da cewa babu wani tsarin karɓa-karɓa cikin jam'iyyar APC face kawai tunani ne da mutane suke ganin hakan ya dace.

"Ina so na gaya muku cewa a kundin gudanarwa na APC, babu wurin da aka ambaci maganar bayar da mulki na shiyya-shiyya. Ina ga dai jam'iyyar PDP ce kawai ke da wannan tunanin.

"Abinda kawai muka sani shine ingancin shugabanci da adalci tare da tafiya da kowa; wannan shine kawai." In ji Shekarau.

Bugu da ƙari, Shekarau ya jaddada cewa alaƙarsa da tsohon gwamna, Rabiu Musa Kwankwaso, da gwamna Abdullahi Umar Ganduje na nan kalau.

Ya ce, "Ni da Ganduje muna tare tsawon shekaru. Lokacin ina famanat sakatare shi kuma lokacin yana Kwamishina, tun can muna mu'amala tare.

"Haka abin yake ni da Kwankwaso; bambancin siyasar mu bai shafi alaƙar mu ba ko kaɗan kuma ban taɓa barin wata jam'iyya zuwa wata ba saboda shi" cewar Malam Ibrahim Shekarau.

Legit.ng ta rawaito cewa tsohon sanata, Kwamred Shehu Sani, ya zayyano wasu abubuwa har 10 da duk wani dan Najeriya zai shiryawa kafin ya shiga siyasa.

Sanata Shehu Sani ya sha kaye a babban zaɓen da ya gabata na shekarar 2019 baya hamayyarsa da gwamna El-Rufa'i ta tilasta shi barin APC.

A cewar tsohon Sanatan, jerin abubuwa 10 shawara ce ga duk wani mutum da ya neme ya ba shi kafin ya tsunduma siyasa.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN