Ba yadda za a yi in yafe mata, Matar aure da kishiya ta babbaka da ruwan zafi


Iklima Musa tana neman a karbar mata hakkinta daga wurin kishiyarta wacce ta watsa mata tafasasshen ruwa a jihar Filato, Linda Ikeji ta wallafa.

Idan za mu tuna, wacce ake zargi da aika-aikar mai suna Justina Peter ana nemanta ido rufe bayan lamarin da ya faru a Gindiri a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.

An gano cewa matar bata taba shiri da Iklima ba tun bayan da mijinta ya aurota a matsayin mata ta biyu a shekaru uku da suka gabata.

Kamar yadda Daily Trust ta bayyana, bayan kishiyoyin sun fara fada, mijinsu mai suna Ate Peter Manomi ya raba su.

Yayin da Iklima ta fito daga dakinta domin kwashe shanyarta, Justina ta watsa mata tafasasshen ruwan zafi.

Wannan harin ya bar Iklima da miyagun kuna a jikinta. Mijinsu Manomi, ya gaggauta mika Iklima asibiti kuma aka kwantar da ita.

"Na duka kasa in kwashe kayana da na wanke, ban san cewa ksihiyata ta taho ba da muguwar niyya. Ban taba tsammanin haka ba saboda an raba mu fadan.

"A lokacin da nake tashi tsaye, ta watsa min ruwa inda na fara ihu. Mijinmu ne ya fara zuwa. Inda nayi sa'a bai yi nisa ba. Da baya kusa da bamu san me zai faru ba." ta bayyana.

A wani labari na daban, 'yan sandan Najeriya sun sake damke mawallafin Sahara reporters, Omoyele Sowore a kan jagorantar wata zanga-zanga da yayi a babban birnin tarayya na Abuja.

Sowore tare da wasu 'yan gwagwarmaya sun shiga hannun 'yan sandan bayan da suka fito zanga-zanga mai suna #CrossoverWithProtest, zanga-zangar da suka shirya a dukkan fadin kasar nan ana gobe sabuwar shekara.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar da suka arce ne suka tabbatarwa da Premium Times cewa an damke Sowore inda aka jefa shi daya daga cikin motocin 'yan sanda bakwai da aka tura wurin zanga-zangar.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN