Kimanin sa'ao'i 24 bayan sanarwa, an yi taron mika mulki daga hannun wanda ya sauka daga karagar zuwa sabon da shugaban kasa ya nada, a yau Alhamis, 28 ga watan Junairu, 2021.
A wannan taro mai kayatarwa da aka gudanar a farfajiyar taron hedkwatar sojin kasa dake birnin tarayya Abuja, Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai, ya mika tutan fara aiki ga sabon shugaban hafsan Sojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru.
Mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina, ya bayyana haka a shafinsa na Tuwita.
A cewar Adesina, Buhari ya nada Manjo Janar Leo Irabor a matsayin shugaban hafsoshin tsaro; Manjo Janar Ibrahim Attahiru matsayin shugaban Sojin kasa; RA AZ Gambo matsayin shugaban sojin ruwa, da kuma AVM IO Amao matsayin shugaban mayakan sama.
A bangare guda, sakamakon sallaman Laftanan Janar Tukur Buratai matsayin shugaban hafsoshin Sojin Najeriya ranar Talata, ya zama babban hafsa mafi dadewa kan kujerar mulki a tarihin Najeriya.
Daily Trust ta bayyana cewa Janar Buratai dan asalin jihar Borno ya yi watanni 66 matsayin shugaban Sojojin kasan Najeriya.
Source: legit
https://chat.whatsapp.com/LKeYYgwzLbW8DdHbjNuEos
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari