Mai martaba sarkin Zuru, Major General Muhammadu Sani Sami na 2 ya bada shawarar cewa ya kamata matan Ciyamomi na yankin Zuru da Kuma kansiloli mata su hada kai da wannan Kungiya domin cigaba da ilmantar da sauran matan cikin gida akan muhimmancin tsabtar abinci domin samun ingantarciyar lafiya ga Al'umma.
Shugaban Karamar hukuma na Zuru Hon Kabiru Turaki, ya raka kungiyar cikin Kasuwa domin fadakarwa akan muhimmancin kula da tsabta ga abubuwan da mu ke ci.
A cikin garin fakai, kungiyar ta samu tarbo na musamman daga Sarkin Fakai Alh Hudu Dan Malam ACP retired. Ya Kuma yi alkawarin za su dauki dukkan matakin da ya dace akan kula da tsabtar abinci.
Shima shugaban karamar hukuma na Fakai, ya yabawa kungiyar game da wannan tunani.
A yankin Danko wasagu, Matar Chairman Hajiya Hussai Sulaiman Shindi, da kuma mataimakin Chairman, sun raka kungiyar zuwa Kasuwa domin fadakarwa da kuma bayarda tallafi.
Daga karshe, kungiyar ta shiga garin Sakaba ta Kuma Sami tarbo na musamman ga Chiefdom na Sakaba Muhammed Sakaba da kuma Ubankasa Mai Diri Alhaji Usman Mai Diri, inda ya gayyato mata a majalisarsa sa domin karbar bayanai a kan tsabtar kula da kayan abinci.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari