Yan bindiga sun kashe 2 daga cikin daliban da suka kwashe, Dalibin da ya kubuta


Daya daga cikin daliban GSSS Kankara na jihar Katsina, wanda ya samu ya tsere daga hannun 'yan ta'adda ya ce 'yan ta'addan sun kashe 2 daga cikin daliban, Vanguard ta wallafa.

Daya daga cikin iyayen yaran da ke hannun 'yan ta'addan, Faiza Hamza Kankara, ta sanar da hakan, inda tace wanda ya tsere daga hannun 'yan ta'addan ne ya sanar dasu hakan.

Matar wacce take cikin matsananciyar damuwa ta ce dalibin ya sanar dasu yadda 'yan bindigan suke ciyar dasu ganye kuma suke dukansu kamar shanu.

'Yan bindiga sun kashe 2 daga cikin daliban da suka kwashe, Dalibin da ya kubuta. Hoto daga @Vanguardngrnews

Ta kara da cewa, dalibin ya ce har yanzu ba a ga fiye da dalibai 500 ba, kuma duk wanda yace yara 10 ne ba a gani ba, karya yake yi.

A cewarta, "Har yanzu ba a ga da na Usman Lawal Tahir ba, wanda yake a SS2.

"Daya daga cikin daliban da ya tsero jiya (Lahadi da daddare) ya ce daliban guda 520 ne, duk da 2 da aka kashe, da shi da ya tsero."

A wani labari na daban, Rundunar sojin Najeriya sun saki wasu hotuna, wadanda suke nuna miyagun makamai da suka kwace daga hannun mayakan Boko Haram lokacin wani karon batta da suka yi a arewa maso gabas a ranar 12 ga watan Disamban 2020.

Kungiyar Boko Haram sun kai wani hari zuwa karamar hukumar Askira Uba da ke arewa maso gabashin Najeriya, sai dai tarkonsu bai kama kurciya ba, a cewar sojojin.

Mataimakin shugaban jami'in hulda da jama'a na Division 7 da ke rundunar sojin Najeriya a Maiduguri, Kanal Ado Isa, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata takarda da ya fitar ranar Lahadi.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN