Zancen tsaro: Zulum ya karba bakuncin wakilan dakarun sojin Kamaru

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya tarba sojoji daga Kamaru a ranar Alhamis. Sojojin sun isa gidan gwamnati da ke Maiduguri, babban birnin jihar. A taron, gwamnan ya bukaci sojojin Kamaru da su taimaka wurin kawo karshen 'yan ta'addan Boko Haram, jaridar Punch ta wallafa. Kwamandan rundunar soji na 4, Janar Saly Mohammadou, ya jagoranci sojojin Kamaru zuwa gidan gwamnatin. Kwamandan Sector 1 Multinational joint Task Force, Janar Bouba Debekreo, Birgediya janar Essoh Jules-Cesar, GOC 7 Div Bridgdier, Janar AK. Ibrahim da sauransu ne suka raka su. A cewar Zulum, sojojin Kamaru sun zo Najeriya ne don su taya sojojin Najeriya wurin yaki da ta'addanci a wuraren tafkin Chadi. Kamar yadda yace, "Mafi yawan mutanen Kamaru da Najeriya suna da al'adu iri daya. Duk da rashin tsaron ya shafin yankin tafkin Chadi, kuma hakan ya shafin tattalin arzikinmu. Shiyasa yakamata mu taru mu yaki rashin tsaro. "Batun siye da siyarwa tsakanin iyaka, dukanmu mun san Banki. Muna iyakar kokarin ganin mun kara bude kasuwar Banki da kuma titunan Banki. Yanzu ya kamata mu bayar da hadin kai wurin kawo karshen rashin tsaro, don jama'a su samu damar yin tafiye-tafiye yadda suka saba." A wani labari na daban, babban malamin addinin musulunci na jihar Kaduna, Dr Ahmad Abubakar Gumi, ya ce rikicin kudancin Kaduna ya dauki lokaci mai tsawo, Daily Trust ta wallafa. A cewarsa, ya zama tilas mutanen kirki, maza da mata, su hada karfi da karfe wurin kawo karshen rikicin addinin. Dr Gumi, wanda shine shugaban KHF ya fara shirin kawo karshen rikicin addini da ke addabar kudancin Kaduna, wanda yake hana cigaba da zaman lafiya. Read more: https://hausa.legit.ng/1389667-taaddanci-zulum-ya-karba-bakuncin-wakilan-dakarun-sojin-kamaru.html

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya tarba sojoji daga Kamaru a ranar Alhamis. Sojojin sun isa gidan gwamnati da ke Maiduguri, babban birnin jihar. 
 
A taron, gwamnan ya bukaci sojojin Kamaru da su taimaka wurin kawo karshen 'yan ta'addan Boko Haram, jaridar Punch ta wallafa. Kwamandan rundunar soji na 4, Janar Saly Mohammadou, ya jagoranci sojojin Kamaru zuwa gidan gwamnatin.

Kwamandan Sector 1 Multinational joint Task Force, Janar Bouba Debekreo, Birgediya janar Essoh Jules-Cesar, GOC 7 Div Bridgdier, Janar AK. Ibrahim da sauransu ne suka raka su. 
 
A cewar Zulum, sojojin Kamaru sun zo Najeriya ne don su taya sojojin Najeriya wurin yaki da ta'addanci a wuraren tafkin Chadi. Kamar yadda yace, "Mafi yawan mutanen Kamaru da Najeriya suna da al'adu iri daya.

Duk da rashin tsaron ya shafin yankin tafkin Chadi, kuma hakan ya shafin tattalin arzikinmu. Shiyasa yakamata mu taru mu yaki rashin tsaro. "Batun siye da siyarwa tsakanin iyaka, dukanmu mun san Banki. Muna iyakar kokarin ganin mun kara bude kasuwar Banki da kuma titunan Banki. 
 
Yanzu ya kamata mu bayar da hadin kai wurin kawo karshen rashin tsaro, don jama'a su samu damar yin tafiye-tafiye yadda suka saba."

A wani labari na daban, babban malamin addinin musulunci na jihar Kaduna, Dr Ahmad Abubakar Gumi, ya ce rikicin kudancin Kaduna ya dauki lokaci mai tsawo, 
 
Daily Trust ta wallafa. A cewarsa, ya zama tilas mutanen kirki, maza da mata, su hada karfi da karfe wurin kawo karshen rikicin addinin. Dr Gumi, wanda shine shugaban KHF ya fara shirin kawo karshen rikicin addini da ke addabar kudancin Kaduna, wanda yake hana cigaba da zaman lafiya.

Source: legit
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN