Fusatattun mutane a unguwar Shataletalen Mile 110 daga karshen titin MKO Abiola a birnin Ibadan, sun kone wani da aka zarge shi da satar babur daga wani dan Acaba ranar Juma'a 4 ga watan Disamba.
Rahotanno sun ce barayin su biyu ne, sun kwace babur a wajen wani dan Acaba sai suka gudu, amma jama'a sun bi su, daya daga cikin barayin ya tsere, amma an kama daya wanda ya sha dan karen duka da sanduna, katako da karafa har da duwatsu. Daga karshe aka banka wa gawarsa wuta.
Wani ganau ya ce barayin sun harbi dan Acaban ne lokacin da yake tsakiyar tafiya kan babur. Lamari da ya ja hankalin matasa da suka rufa wa barayin baya ta hanyar binsu da gudu har aka kama daya daga cikinsu.
Kakakin yansandan jihar Oyo SP Olugbenga Fadeyi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata takarda da ya raba wa kafofin labarai. ranar Juma'a 4 ga watan Disamba.
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari