Yan sanda sun kubutar da attajiri da kidnapa suka sace a Jega bayan barin wuta da bindigogi


Jami'an yansandan jihar Kebbi da ke karamar hukumar Jega, sun yi artabu da yan bindiga da suka sace wani mutum mai suna Alhaji Shehu Umar mai shekara hamsin da biyar a kauyen Kolonkoji da karfe 1:50 na dare, suka harbi makwabcinsa mai suna Mustapha Ahmed a kafa kuma suka tafi da Alhaji Shehu.

Sai dai bayan yan sanda reshen Jega sun sami rahotu, jami'an sun bi sawun masu garkuwa da mutanen kuma suka samesu aka yi artabu na harbe harbe da barin wuta da bindigogi tsakanin masu garkuwa da mutanen da jami'an yan sanda. 

Sakamakon haka masu garkuwa da mutane suka tsere suka bar Alhaji Shehu. Yan sanda sun mayar da Alhaji Shehu zuwa wajen iyalinsa, yayin da aka garzaya zuwa Asibitin FMC Birnin kebbi da makwabcinsa Mustapha da masu kidnapa suka harba a kafa domin samun kulawan Likitoci.

Kwamishinan yansandan jihar Kebbi CP Ogunbiade Oluyemi Lasore ya sha alwashin taka wa masu aikata miyagun ayyuka burki a jihar Kebbi. Kwamishinan ya yi wannan bayani ne a wata takarda da aka raba wa kafofin watsa labarai a jihar Kebbi wanda ke sanye da hannun Kakakin hukumar yansandan jihar Kebbi DSP Nafi'u Abubakar ranar 2 ga watan Disamba, amadadin Kwamishinan yansandan jihar.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN