Hukuncin kisa saboda kashe mijinta: Maryam Sanda za ta daukaka kara zuwa Kotun koli


Maryam Sanda ta na shirin daukaka kara zuwa Kotun koli ta Najeriya bayan Kotun daukaka kara ta jaddada hukuncin Kotun tarayya na kisa ta hanyar ratayewa har ta mutu bayan Kotun ta same ta da laifin kashe mijinta Bilyamin Muhammed.

Ranar Juma'a 4 ga watan Disamba ne wata Kotun daukaka kara a birnin Abuja ta jaddada hukuncin kisa da Kotun tarayya ta yanke mata.

A shekata ta 2017, rikicin cikin gida ya kaure tsakanin Maryam da mijinta Bilyamin, inda ake zargin ta yin amfani da wuka ta caka masa a wurare da dama, lamari da ake zargin ya yi sanadin mutuwarsa.

Jim kadan bayan jaddada hukuncin a Kotu, Lauyan Maryam Sanda mai suna Joe  Gadzama SAN, ta ce za su daukaka kara zuwa Kotun koli, Kotun daga ke sai Allah ya isa a Najeriya.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN