JNI ta fallasa wadanda basu son a kawo karshen rashin tsaro a Najeriya


Kungiyar musulunci ta Najeriya, wacce Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, CFR, mni, Sarkin Sokoto yake jagoranta ta ce ta samu mummunan labari wanda ya dimauta ta na satar daliban GSSS, Kankara, jihar Katsina, bayan harbin jami'an tsaron a bakin makarantar da misalin karfe 10:45pm a ranar Juma'a.

Dr. Khalid Abubakar Aliyu, babban sakataren JNI, a wata takarda, ya ce wannan daya ne daga cikin miyagun hare-haren da 'yan ta'adda suka kai, bayan kisan Zabarmari da ya auku babu dadewa, Vanguard ta ruwaito.

"Wannan ya kara tuna mana da satar 'yan matan Chibok da na Dapchi na jihar Borno da Yobe a arewa maso gabacin Najeriya, kuma hakan fami ne a kan ciwo."


JNI ta fallasa wadanda basu son a kawo karshen rashin tsaro a Najeriya. Hoto daga @daily_trust

"Za mu cigaba da tambaya: Yaushe ne talakawa za su cigaba da rayuwa cikin tsaro? Yaushe ne gwamnatin tarayya da na jihohi za su cigaba da sukar ta'addanci ba tare da daukar mataki ba? Shin gwamnati da jami'an tsaro sun dimauce ne ta yadda basa iya kulawa da rayukan al'umma?

"Shin akwai wasu sirruka ne da gwamnati take boye wa jama'a? Irin wadannan tambayoyin za su cigaba da yawo a zukatan 'yan Najeriya da sauran jama'a. Al'umma za ta cigaba da was-wasi a kan gwamnati."

"Abin ban mamaki a nan shine yadda aka kai hari cikin jihar kuma a lokacin da shugaban kasa yake cikinta.

"Shin 'yan ta'addan har sun samu kwarin guiwar kai hari a gaban gwamnati ko kuma jami'an tsaro kenan? Hakan yana nuna cewa kwannan 'yan bindiga za su fara mulkar wasu garuruwa kuma su dinga yin yadda suka ga dama.

Alamu sun nuna cewa akwai manyan jami'an tsaron da ba su son wannan tashin hankalin ya kare kenan.

Yace idan har 'yan bindigan sun je da baburansu har suka kwashe daliban, ta yaya za a yi har su gama wucewa amma jami'an tsaro ba su gano su ba? Ya aka yi 'yan ta'addan suka dauki tsawon lokaci suna kwashe yaran, kuma suka tsere dasu ba tare da an sani ba?

A wani labari na daban, a kan taron APC NEC, gwamnonin jam'iyya mai mulki sun yi wani taro a ranar Litinin da yamma, inda suka tattauna a kan makasudin taron da za a yi na NEC.

A taron, Premium Times ta gano cewa gwamnonin sun hada kai a kan hana shugaban kasa Muhammadu Buhari zaunawa da 'yan majalisar tarayya a kan batun rashin tsaron da ke kasar nan.

Sun ce hakan zai iya janyo wa shugaban kasa raini, ta yadda 'yan majalisar tarayya za su dinga kiransa taro a kan kananun abubuwa.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN