Yadda babban mota dauke da kayan nauyi ta murkushe direban Keke napep har lahira


Wata babban mota dauke da kayan nauyi, ta murkushe wani bawan Allah har lahira da sanyin safiyar Juma'a 4 ga watan Disamba bayan ta kade shi kuma ta bi ta kanshi ta take shi a gaban kasuwar Slaughter Market da ke Eliozu a kan hanyar East West Road.

ISYAKU.COM ya samo cewa wanda motar ta take, direban Keke-Napep ne da ke kokarin ketare titi kafin motar ta bugeshi ta murkushe shi. Mun samo cewa direban babban motar mai jan kala ya yi kokarin tserewa, amma jama'a suka cafke shi.


Fusattattun jama'a sun yi kokarin halaka shi, amma wasu daga cikinsu sun dage wajen ganin an mika shi ga yansanda.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN