An cire Wiwi a cikin jerin ababe da aka haramta amfani ko tuammali da su a dokokin tarayya na kasar Amurka.
Wannan shi ne karo na farko da Majalisar Wakilan Amurka ta kada kuri'a kan cewa abu ne da za a iya cirewa daga cikin miyagun kwayoyi a dokokin tarayya..
Yan Majalisar Wakilan kasar Amurka sun kada kuri'a 228 da rinjaye wadanda suka goyi bayan cire Wiwi daga jerin haramtattun ababen tu'ammali, yayin da wadanda ke son a bar Wiwi cikin haramtattun ababe da ake tu'ammali da su suka kada kuri'a 164.
Jihohi goma sha biyar tare da gundumar Colombia sun halatta tu'ammali da Wiwi, yayin da jihohi 12 suka jaye haramci kan tu'ammali da Wiwi tare da samar da damar amfani da Wiwi domin harkar kiwon lafiya.
A jihohi shida ne kawai amfani da Wiwi ya haramta a Amurka a halin yanzu.
Jihohin Arizona, New Jersey, Montana, da South Dakota sun kada kuri'ar halatta Wiwi ranar 3 ga watan Nuwamba.
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari