Kotun daukaka kara ta jadda hukuncin kisa ga Maryam Sanda sakamakon kashe mijinta


Wata babban Kotun daukaka kara abirnin Abuja Najeriya ta jaddada hukuncin da wata Kotu ta yanke wa Maryam Sanda bayan ta same ta da laifin  kashe mijinta Bilyamin Muhammed.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta gurfanarda Maryam Sanda a gaban Kotu bisa tuhumar kashe mijinta Bilyamin dan gidan tsohon shugaban jam'iyar PDP ta kasa bayan wani hargitsin cikin gida da ya auku tsakanin Maryam da Bilyamin wanda ake zargin Maryam ta yi amfani da wuka ta kashe Bilyamin. a 2017.

Kotu ta yanke wa Maryam hukuncin kisa ta hanyar ratayewa har sai ta mutu bayan Kotu ta kamata da laifin tuhumar da ake yi mata.

Sai dai Maryam ta daukaka kara zuwa Kotun daukaka kara, wadda ta jaddada hukuncin Kotu na baya kan hukuncin kisa ga Maryam Sanda ta hanyar ratayewa.Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN