Tsoron shugaba Buhari kuke yi, Shehu Sani ga 'yan majalisar wakilai


Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce 'yan majalisar wakilai suna tsoron shugaba Muhammadu Buhari, shiyasa suka soke gayyatar da suka yi masa.

Sani ya yi wannan maganar ne da BBC Hausa, inda yace ya kamata shugaba Buhari ya bayyana gaban majalisar don amsa tambayoyi a kan matsalolin tsaron dake addabar Najeriya.

A cewarsa, babu dalilin da zai sanya a ce su gayyaci Buhari kuma su koma su canja ra'ayi.

"Ana ta kashe mutane a kowacce rana, ana ta garkuwa da dubbannin jama'a dare da rana kuma alamu sun nuna cewa shugaban kasa bai damu ba. Wadannan suna cikin dalilan da suka sanya aka maka Jonathan da kasa.

"Menene amfanin fasa gayyatar shugaban kasa? Hakan yana nuna kuna tsoron shi ne. A kalla gayyatar za ta sanya shugaban kasa yayi wa 'yan Najeriya bayani su san matakan da yake kokarin dauka," yace.

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bada labarin yadda Janar Olu Bajowa mai ritaya ya ceci rayuwarsa inda ya tsallake mutuwa daga hannun Buka Suka Dimka a juyin mulkin 1976.

Obasanjo ya ce da Bajowa bai gayyacesa sunan dan sa ba, da tuni sojoji masu juyin mulki sun hallaka shi har lahira.

Tsohon shugaban kasan ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 27 ga watan Disamban 2020 a jihar Ondo yayin biki

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN