Jarumar budurwa mai POS ta cafke yan fashi 2 a shagonta


Wata jarumar budurwa mai sana'ar POS ta yi bajinta wajen kwatar kanta daga yan fashi da makami guda biyu a karamar hukumar Uhogwa Ovia na arewa maso gabas a jihar Edo.

ISYAKU.COM ya samo cewa yan fashin masu suna Andrew Adubu da Destiny Olu sun bukaci budurwar ta basu kudi daga wajen sana'arta na POS, sai dai lokacin da ta zura katin ATM da suka kawo a na'urar POS, sai suka zaro bindigar hannu kirar gida watau Pistol suka nuna mata cewa dole ta basu duk kudadenta da wayoyinta na salula.

Ana cikin haka ne sai ta buge hannun wanda yake rike da bindiga kuma bindiga ta fadi a kasa, sakamakon haka budurwar ta yi kururuwa nan take jama'a suka kawo mata dauki aka kama yan fashin.

Kakakin yan sandan jihar Edo SP Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce wadanda aka kama sun tabbatar wa yan sanda lokacin bincike cewa sun aikata laifin.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari