An tsige shugaban karamar hukumar Shiroro bisa zargin almundahana


Kwamred Suleiman Dauda Chukuba, shine tuɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Shiroro da aka sauke daga kan kujerarsa.

An tsige shi bisa zargin cire kuɗaɗe tare da murƙushe harajin ƙaramar hukuma ba tare da samun sahalewa daga ƴan majalisar su ba, kamar yadda Vanguard ta rawaito ranar Talata.

Sannan kuma ya yi almubazzaranci da kuɗaɗe.

Mambobi goma sha ɗaya daga cikin Kansiloli goma sha huɗu sun kaɗa kuri'ar tsige shugaban ƙaramar hukumar.

Wasu ƙarin zarge-zarge da ake yiwa Shugaban ƙaramar hukumar sun haɗar da kashe kuɗaɗen harajin ƙaramar hukuma ba tare da samun sahalewar majalisar Kansiloli ba, almubazzaranci da sauransu.

Sauran sun haɗar da laifukan almundahanar kuɗaɗe, ƙin gurfana gaban majalisa na tsawon shekara guda don bayanin ƙiyasin haraji da adadin kuɗaɗen da ƙaramar hukuma ta samu.

Sun ƙara zargin cewa bayan samun sahalewar cire ₦7,000000 daga asusun ƙaramar hukuma don shiryawa musu taron sanin makamar aikin bita, an shafe tsawon watanni huɗu, amma har yanzu bulumbuƙwui, babu wani labari ko batu kan kuɗaɗen.

Shugaban ƴan majalisa, Malam Yusuf Aliyu, shine ya jagoranci zaman tare da mambobin majalisar 14.

Ƴan majalisar su 14 sun nufi gidan gwamnati dake Minna bayan zartar da hukuncin don shawara da wasu ƙusoshin gwamnati akan batun.

An kasa samun tuɓaɓɓen ƙaramar hukumar don maida martanin kare kansa daga zarge-zarge da ake yi masa

A ranar Talata ne Legit.ng ta rawaito cewa NCDC, cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa, ta ce 'yan Nigeria su shirya girbar sakamakon uwar watsi da suka yi da matakan dakile yaduwar annobar korona

Shugaban NCDC, Dakta Chikwe Iheakwezu, ya ce 'yan Nigeria su shirya domin za'a fuskanci hauhawar alkaluman masu kamuwa da cutar korona daga satin nan da muke ciki.

A cewar NCDC, makon da ya gabata ya kasance daga cikin mafi ban tsoro saboda tashin gwauron zabi da alkaluman mutanen da suka kamu da cutar ya yi.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN