Ta yaya ake warkewa daga cutar HIV?


A fadin duniya an ware ranar daya ga watan Disamba, a matsayin ranar wayar da kai kan cutar AIDS ko Sida a duniya.

Majalisar dinkin duniya ta ce rana ce da duka kasashen duniya za su hada kai don nuna goyon baya ga mutane masu fama da wannan cuta ta AIDS, sannan a tuna da mutanen da suka rasa rayukansu dalilin wannan cuta.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa mutum miliyan 38 ne ke rayuwa da cutar a duniya.

Sannan mutum miliyan daya da dubu dari bakawi ne suka kamu da cutar a wannan shekarar. Sai dai ta ce akwai wasu mutum sama da miliyan 25 da ke da damar amfani da magungunan cutar Aids.

Cutar Aids kan samu ne idan kwayar cuta ta HIV ta shiga jikin mutum ta raunana garkuwar jikinsa. Idan garkuwar jiki ta yi rauni, mutum zai yi saurin kamuwa da wasu cutukan Kaman cutar TB da wasu nau'ukan daji.

Ana kammuwa da cutar HIV ne ta hanyar saduwa ko ta jini. Misali amfani da allura ko reza ko wani abu mai tsini da mai dauke da cutar ya yi amfani da shi ya yanke. Ko ta rauni ko a jiki.

Sai dai a shekarun baya, kwararru sun samar da magungunan da ke hana kwayoyin cutar HIV bunkasa a jikin mai dauke da ita.

Alamomin cutar HIV

Mafi yawan mutanen da su ka kamu da cutar HIv kan ji alamomin mura musamman makonni biyu zuwa shidda bayan daukar cutar. Bayan wannan, bincike ya nuna ba lallai a sake ganin wasu alamomi ba har sai bayan shekaru masu yawa.

Alamomin da aka fi gani a masu fama da cutar sun hada da:

 • Zazzabi
 • Ciwon wuya
 • Kuraje a jiki
 • Kasala
 • Ciwon gaɓoɓi
 • Kaluluwa a wasu sassan jiki

Bayan waɗannan alamomin na farko-farko sun ɓace, ba lallai a sake ganin wasu alamomi ba.

A wannan lokaci, ƙwayar cutar tana ci gaba da lalata garkuwar jiki.

Da zarar garkuwar jiki ta durƙushe, alamomin da za a iya ji su ne:

 • Rama
 • Gudawa ba ƙaƙƙautawa
 • Zufa cikin dare
 • Yawan ƙuraje a jiki
 • Manyan cututtuka masu haɗari

Gano cutar HIv a kan kari na rage yiwuwar lalacewar garkuwar jiki.

Sannan a shekarun baya, kwararru sun samar da magungunan da ke hana kwayoyin cutar HIV bunkasa a jikin mai dauke da ita. 

BBCHausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN