Matata tana kwanciya da makabci na, mijin da ya nemi kotu ta raba auren sa ya bayyana


Wani direban tasi, Kazeem Hamzat, ya bayyanawa kotun gargajiya ta Mapo a Ibadan, da ta raba auren shekara 21 tsakanin sa da matarsa, Mujidat bisa zargin cin amanar aure, Daily Nigerian ta ruwaito.

Hamzat ya shaidawa alkalin kotun Ademola Odunade da sauran alkalan Alhaji Sulaiman Apanpa da kuma Alhaji Rafiu Raji cewa rayuwar sa ta na cikin hadari matukar ya ci gaba da zama da Mujidat.


Matata tana kwanciya da makabci na, mijin da ya nemi kotu ta raba auren sa ya bayyana. Hoto: @Vanguardngr

Da ya ke jawabi, mutumin mai yaya biyar da yake zaune a Odo Oba da ke Ibadan, ya ce ya sha kama Mujidat a wani irin yanayi da wani makwabcinsa da wasu mazan ma daban.

"Wata rana bazan manta ba, na dawo daga aiki sai Mujidat take cewa ya kamata mu nemi wani É—akin haya don karawa akan wanda muke dashi.

"Na nuna rashin amincewa akan dalilin da ta bani, amma a haka na yarda saboda ban san bukatar ta ba.

Bayan yan kwanaki, na tashi tsakar dare saboda sautin muryar wata mata a kusa da gidan mu, kuma na yanke shawarar duba me yake faruwa.

"Na duba sabon dakin in da matar ta wa take kwana, amma sai na ga bata nan.

"Sai na lura muryar na fitowa daga dakin wani gwauro da ke makwabtaka da mu, kuma na buga kofa fiye da awa daya ba wanda ya bude.

"Sauran makwabta ne suka ce in hakura in barwa Allah.

"Hakan ta ci gaba da faruwa kuma Mujidat ta ce min zan kashe kaina matukar na ci gaba da bibiyar harkokinta. "

Da take maida martani, Mujidat mai aikin share ta karyata zargin, ta kuma bayyana mutumin da mijin ta yake magana a matsayin wanda ba zai iya kwanciya da mace ba.

Da kotun ta bukaci karin bayani, Mujidat ta tabbatar da cewa ba shi da karfin kwanciya da mace saboda "mahaifiyar mutumin ta ce dan ta bashi da lafiya kuma ba zai iya kwanciya da mace ba.

"Hamzat mugun mutum ne wanda bai taba yarda dani ba. Ya saka min "mugun" (wani maganin gargajiya na kama masu cin amanar aure) a wurare daban daban."

Da kotu take yanke hukunci, ta raba auren saboda kar abin ya kai ga babbar barna.

Daga cikin yaran su biyar an bawa Hamzat manyan su uku, ragowar biyu kuma aka baiwa Mujidat.

Haka kuma Hamzat zai dinga bawa Mujidat naira 6,000 a matsayin kudin ciyarwa kuma zai dauki nauyin karatun su.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN