Sayyada Maryam diyar shugaban darikar Tijjaniyya ta rasu


Sayyada Maryam Sheikh Ibrahim Inyass, diya wurin shugaban darikar Tijjaniyya, Sheikh Ibrahim Inyass, ta rasu a kasar Senegal kamar yadda Daily Trust ta tabbatar.

Marigayiya Maryam ta kasance mai hidima tare da sadaukar da rayuwarta wajen harkokin da suka shafi addinin Musulunci, lamarin da ya sa ake mata lakabi da 'Hadimar Qur'ani'.

A nan gida Najeriya, annobar cutar korona ta zama sanadiyyar mutuwar tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom a karkashin mulkin soja, Air Commodor Idongesit Nkanga, a ranar Alhamis, kamar yadda NewswireNGR ta rawaito.

NewswireNGR ta rawaito cewa gidan talabijin na Channels ya wallafa cewa tsohon gwamnan ya rasu yana da shekaru 68 a wani asibiti da ke Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom. Ba'a bayyana sunan asibitin ba.

Marigayi Nkanga ya kasance gwamnan jihar Akwa Ibom daga watan Satumba na shekarar 1990 zuwa watan Janairu na shekarar 1992 a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB).

Kafin rasuwarsa, marigayi Nkanga ya na rike da shugabancin kungiyar kishin yankin kudu maso kudu, Neja-Delta (PANDEF).

A ranar Juma'a ne Legit.ng ta rawaito cewa Allah ya yi wa majidadin Kano kuma makaman masarautar karaye, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, rasuwa.

Marigayi Musa Saleh ya kasance mahaifi wurin tsohon gwamnan Kano kuma tsohon sanata, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso

Za'a yi jana'izarsa da misalin karfe uku na ranar Juma'a a unguwar Bompai da ke cikin birnin Kano.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN