Manyan 'yan siyasa 10 da ke son maye gurbin Buhari


A halin yanzu shekaru biyu da watanni kalilan suka rage zaben 2023. Tuni fitattun 'yan siyasa daga jam'iyyun APC da PDP suka fara kamfen domin maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Yayin da kamar su Sanata Ahmed Yarima ne kadai suka bayyana burinsu, sauran suna ta amfani da makusantansu don bayyana burinsu.

A yayin da muke shiga 2021, akwai tsammanin cewa zawarcin kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tsananta daga dukkan manyan jam'iyyun siyasa biyu na Najeriya.

Manyan 'yan siyasa 10 da ke son maye gurbin Buhari

Manyan 'yan siyasa 10 da ke son maye gurbin Buhari. Hoto daga @daily_trust

Ga manyan 'yan siyasa 10 da ke zawarcin kujerar shugaban kasan:

1. Atiku Abubakar

Ya yi mataimakin shugaban kasan Najeriya daga 1999 zuwa 2007 yayin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Shi ne dan takarar shugaban kasa a zaben 2018 karkashin PDP inda ya sha mugun kaye hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari na APC.

Atiku dan kasuwa ne babba kuma dan siyasa ne wanda ake ganin siyasarsa ta watsu a kasar nan ne sakamakon karfin aljihunsa.

2. Bola Ahmed Tinubu

Jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu bai bayyana burinsa karara ba amma makusantansa da magoya bayansa sun fara yakin neman zabensa.

Duk da Tinubu tsohon gwamnan jihar Legas ne, ya jaddada cewa yanzu lokacin yakin neman zabe bai yi ba amma na kusa da shi sun fara.

3. Rotimi Amaechi

Ba da dadewa ba, Rt. Hon Rotimi Amaechi, tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ministan sufuri a halin yanzu ya jaddada cewa akwai bukatar APC ta mutunta yarjejeniyar mulkin karba-karba da tayi da kudu.

Wannan lamarin ne ya bayyana cewa yana da burin hawa wannan kujerar ta shugabancin kasa.

Amaechi yana daya daga cikin ministocin Buhari da ake ganin ayyukansu tare da jin muryarsa a wannan gwamnatin.

Ya yi darakta janar na kamfen din Buhari a 2015 da 2019. Yana da gogewa a matsayin wanda yayi kakakin majalisar jihar Ribas, gwamnan jihar sau biyu, tsohon shugaban NGF kuma yanzu ministan da ke jagorantar babbar ma'aikata.

4. Kayode Fayemi

Duk da Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti bai bayyana burinsa na shugabancin kasa a 2023 ba, tsokacin da wani jigon APC a jiharsa yayi yasa aka shinshino hakan.

5. Rabiu Musa Kwankwaso

Akwai manyan alamu da ke nuna cewa Sanata Rabiu Kwankwaso na jihar Kano zai nemi kujerar shugabancin kasar nan.

Duk da tsohon ministan tsaron bai bayyana burinsa ba karara, ya nema tikitin takarar a PDP da APC amma duk bai yi nasara ba.

Kwankwaso wanda fitaccen dan siyasa mai tarin magoya baya a Kano, shine shugaban kungiyar Kwankwasiyya.

6. Ahmed Sani Yarima

Ya hau kujerar gwamnan jihar Zamfara daga 1999 zuwa 20017. Ya wakilci yammacin Zamfara a majalisar dattawa kuma ya yi mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar.

Yarima ne mutum daya da ya bayyana burinsa na gadar kujerar shugaba Buhari a 2023. Ya yi wannan yunkurin a 2007 amma ya janye tare da goyon bayan Buhari.

7. Aminu Waziri Tambuwal

Gwamnan jihar Sokoton ya hau kujerarsa a 2015 ta jam'iyyar APC. Yana daya daga cikin masoman jam'iyyar amma daga bisani sai ya bar ta kwata-kwata.

Ya nemi tikitin takarar shugaban kasa da Atiku a PDP inda daga bisani ya koma Sokoto ya karba tikitin takarar gwamnan jihar, lamarin da yayi nasara.

8. Yahaya Bello

Akwai manyan alamu da ke nuna cewa Yahaya Bello na jihar Kogi na daya daga cikin masu hango kujerar shugaba Buhari a 2023.

Tuni dai aka saka manyan allunan kamfen a jiharsa inda ake bukatarsa da ya fito neman kujerar shugaban kasa a 2023.

9. David Umahi

Gwamnan David Umahi na jihar Ebonyi yana daya daga cikin 'yan siyasan Kudu maso gabas da ake tunanin suna son maye gurbin Buhari a 2023.

Ba da dadewa ba ne Umahi wanda jigo ne a jam'iyyar PDP ya koma jam'iyyar APC a wani salo na shi na samun damar takarar.

Duk da Umahi ya ce sauya shekarsa bashi da wata alaka da burinsa na zama shugaban kasa a 2023, masana siyasa sun sakankance cewa bai fadi gaskiyar abinda ke ransa ba.

10. Bala Mohammed

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi tsohon mininstan ABuja ne daga 2010 zuwa 2015.

Sanata Mohammed na jam'iyyar PDP ya kayar da gwamnan APC a 2019 wanda ya so zarcewa, lamarin da ya kawo babban nakasa ga jihar da aka san ta da zaben shugaban Buhari.

Gwamnan bai bayyana bukatarsa ba amma wata kungiya da ke Abuja ta fara kira garesa da ya fito.

A wani labari na daban, daga bakin wasu daga cikin yaran makarantar Kankara da aka sace, sun tabbatar da cewa an biya kudin fansa kafin a sakesu, mujallar The Wall Stree ta tabbatar.

Akasin ikirarin gwamnatin tarayya da cewa babu sisin kwabo da aka biya domin kubutar da dalibai 334 daga hannun 'yan bindiga.

A wani rahoton ranar Laraba, WSJ ta ce uku daga cikin daliban da aka sace sun tabbatar da cewa an biya kudi kafin a sakesu.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN