Gwamna Abubakar Atiku Bàgudu ya ba mata masu sana'ar sayar ka kayan miya tallafin N6.15m ranar Lahadi a garin Birnin kebbi.
Mai taimaka wa Gwamna Bagudu kan harkar labarai Yahaya Sarki, ya ruwaito cewa mata 205 ne suka amfana da kudin tallafin inda kowace mace ta Sami N30.000.
Gwamna Bàgudu ya sanar da bayar da tallafin ne a wajen taron yaye wadanda suka sami horo kan yadda za su adana kayakin miya masu saurin lalacewa, wanda aka gudanar a Kasuwar Bayan Kara a garin Birnin kebbi ranar Lahadi.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari