Samari 11 yan jihar Jigawa sun mutu kan hanyar zuwa Kano rubuta jarabawan shiga Navy


Matasa 11 sun rasa ransu sakamakon hatsarin mota yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa rubuta jarabawar shiga sojin ruwa NAVY a birnin Kano tarayyar Najeriya.

Matasan sun rasa ransu ne bayan motar da suke tafiya a ciki ta ci karon bazata da wata motar Tilera da ta tsaya a kan kan titi ba daidai ba ranar Asabar12 ga watan Disamba.

Wadanda suka rasu sun fito ne daga karamar hukumar Gagarawa na jihar Jigawa kamar yadda bayanin yansanda ya nuna.


Wani ganau ba jiyau ba ya ce lamarin ya faru ne a garin Ringim na jihar Jigawa kilomita 70 zuwa birnin Kano, inda suke haramar zuwa domin su rubuta jarabawar shiga NAVY.

Ya kara da cewa motar da matasan ke ciki kirar Gulf wagon, ta ci karon bazata ne da wata mota kirar Tilera da ke dauke da rake, kuma a ajiye ta a kan hanya ba daidai ba.

Kakakin hukumar yan sandan jihar Jigawa SP. Abdul Jinjiri, ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa da Shelkwatan yansandan jihar ta fitar ranar Asabar.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN