Soji sun kama shugaban jam'iyar PDP na Igbide Ward a karamar hukumar Isoko ta yamma mai suna Christopher Irivi-Ubulubu, sakamakon mallakar bindiga da albarusai ba bisa ka'ida ba.
Wannan ya biyo bayan wani rikici ne da ya barke tsakanin al'umman Igbede da Emede a karamar hukumar Isoko ta yamma wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutum biyar. Kazalika an lalata dukiya da dimbin Naira.
An kama wannan shugaban ne dumudumu dauke da bindiga a motarsa yana kokarin kai hari a makwabta sakamakon rikicin da ya samo asali daga rigimar fili.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari