Matata ta tare da wani namiji a barikin mu, sojan mai ritaya ya shaidawa kotu


Wani sojan sama mai ritaya dan shekara 39, Richard Imana ya roki wata kotun gargajiya a Iyana-Ipaja da ke jihar Lagos da ta raba aurensa, saboda wulakanta shi da hana shi ganin yayansa da matar sa ke yi. Richard ya shaidawa kotu cewa matarsa, 

Nkem, ta bar gidan auren ta, ta kuma bi wani mutumin a barikin da ya ke zaune da iyalansa. Ya ce matar ta koma wajen mutumin lokacin da shi ya ke aiki a Borno, Vanguard ta ruwaito.

"Matata ta rufe bangare na, ta tare a gidan wani lokacin ina Borno. Ta guje ni saboda wani, nayi murabus don kula da yayanmu. "Akwai lokacin da bani da lafiya likita ya bukaci ta sanya hannu a takardu don ayi min magani amma ta ƙi. " Ta hana ni ganin yara na, ta dauke karamin ta kaiwa mahaifiyar ta ba tare da izini na ba," a cewar mai karar.

Da take maida martani, Nkem mai shekara 34 ta ce ita fa ba wajen wanda ta koma, ta je wajen kawarta ne wadda ta ke makwabciyar ta saboda mijin ta ya daina tura mata kudin abinci. 

"Na kai yaya na kauye lokacin da hakan ke faruwa saboda mahaifinsu baya turo kudin abincin su. "Na kwashe kaya na cikin fushi, saboda lokacin, albashi na N25, 000 kuma bazai isa ni da yara ba," a nata jawabin.

Ta ce ya shigar da karar ne a bisa rashin fahimta. Sai dai duk ma'auratan biyu sun bayyana cewa har yanzu su na kaunar junansu sai dai kawai rashin samun lokacin tattaunawa. Alkalin kotun, Prince Adewale Adegoke ya gargadi Nkem kan tarewa tare da kawar ta.

Ya kuma umarci a dawo da karamin dan su Lagos a kuma hada shi da baban shi. Adegoke ya ce su zauna lafiya ya kuma dage cigaba da sauraron ƙarar zuwa 15 ga Disamba don daukar mataki

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugaban hukumar daukan ma'aikata, Dakta Nasiru Mohammed Ladan Argungu daga mukaminsa. 

Sanarwar saukewar na kunshe ne cikin wata wallafa da babban mataimakin shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta ce Buhari ya umurci karamin ministan Kwadago da Ayyuka, Festus Keyamo, SAN, ya nada shugaban riko daga cikin manyan direktocin hukumar don maye gurbin Argungu a yanzu.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN