Bidiyon yadda Maina ya yanke jiki ya fadi a kotu


An kwashi dirama da 'yan kallo a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja yayin da Abdulrasheed Maina ya yanke jiki ya fadi bayan gurfanarsa a ranar Alhamis. 

A wani lokaci can a baya, Maina ya taba yanke jiki ya fadi a harabar kotu, lamarin da yasa ya koma zuwa kotun a kan keken guragu, kamar yadda TheCable ta wallafa. Sai dai, bayan an bayar da shi beli, Maina ya mike, ya sulale, ya gudu ya bar Nigeria kamat yadda ya taba yi a baya.

Maina, tsohon shugaban hukumar fansho (PRTT), ya shaidawa babbar kotun tarayya a Abuja cewa babu wata tuhuma da zai amsa akan zarge-zargen da Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta ke yi masa.

Maina ne ya faɗawa babban alƙalin kotun, Okon Abang, hakan jim kaɗan bayan EFCC ta rufe shari'ar, ta bakin lauyanta, Farouk Abdullahi, a ranar Laraba.

Ya ce kundinsa da kimarsa zasu kasance ba tare da kowanne irin tabo ba nan ba da jimawa ba domin gaskiya za ta bayyana. Duk da cewar ana tuhumarsa da laifuka 12 da suka shafi almundahanar kuɗaɗe da suka kai kimanin Naira biliyan ₦2b, Maina ya yi iƙirarin cewa bai aikita ko ɗaya cikin laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa ba.

An dawo da Maina ga hukumomin Najeriya bayan kama shi a jamhuriyyar Nijar a ranar Litinin. Ya tsallake beli wanda ya kai ga kama Sanata mai ci, Ali Ndume, wanda ya tsaya masa a kotun kafin a bayar da shi beli. 

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa jami'an binciken sirri da hadin gwuiwar na hukumar yaki da cin hanci sun kama Abdulrasheed Maina a Jamhuriyar Nijar a ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba. Kamfanin dillancin labarai na PRNigeria ya ce an kama Maina a wani gari da ke cikin Jamhuriyar Nijar.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN