Gwamnoni da Jam'iyya na da hannu wajen sa Shugaban kasa watsi da gayyatar Majalisa


A wajen taron gaggawa na NEC da jam’iyyar APC mai mulki ta yi, an kawo maganar zuwan shugaba Muhammadu Buhari zuwa zauren majalisa. A baya an shirya cewa shugaban kasar zai bayyana a gaban ‘yan majalisar tarayya domin ya yi masu bayanin abin dake faruwa game da sha’anin tsaro.

Wani fitaccen gwamna daga yankin Kudu ya tasa shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, a gaba a kan gayyatar da suka aika wa shugaban kasa. 

 

Wannan gwamna na APC ya nemi jin dalilin da ya sa Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya ba ‘yan majalisar dama cewa shugaban kasa ya bayyana a gabansu. Femi Gbajabiamila ya ce shugaban kasar ya na da damar ya hallara a zauren majalisar ko ya ki.

Jaridar Premium Times da Arise su ka ce a nan aka ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarar ya yi fatali da wannan goron gayyata na majalisa. 

A gefe guda kuma, gwamnan jihar Yobe wanda shi ne shugaban rikon-kwarya na APC, Mai Mala Buni, ya ce sun cin ma matsaya a game da wannan magana. Mai Mala Buni ya ce jam’iyya ta yarda cewa shugaban kasa ba zai bayyana gaban ‘yan majalisa ba.

Wannan bai yi wa ‘yan majalisar APC da ke taron dadi ba. Gwamnonin jam’iyyar APC sun ce sun samu labari cewa ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP za su yi amfani da wannan dama ne su ci mutuncin shugaban kasar. Dazu kun ji cewa wani daga cikin jiga-jigan jam'iyyar APC ya yi magana game da wannan batu, ya ce ba shugaban kasa ya kamata ya saurari 'yan majalisar ba.

Farouq Adamu Aliyu ya bayyana cewa bai kamata Buhari ya amsa gayyatar majalisar da kansa ba, ya ce wannan aikin manyan hafsoshin tsaron kasar ne. Jigon na APC uma tsohon 'dan majalisar Jigawan ya ce Buhari ba mai son yawan surutu ba ne.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN