Matashi ya rataye kanshi har ya mutu sakamakon wani dalili, duba abin da ya faru

aAAAA

Wani matashi ya rataye kanshi har ya mutu a karamar hukumar Urtta Owerri ta gabas a jihar Imo da safiyar Lahadi 20 ga watan Disamba.

Ya rataye kanshi ne a wata itaciya da ke daga bayan harabar gidanshi.

Babu wani bayani ko alamu da suka bayyana kafin matashin ya kashe kanshi.

Ana ci gaba da samun yawaitan mutane da ke kashe kansu a watanni shida da suka gabata a Najeriya.

A kwanakin baya, mun kawo maku labari da hotunan yadda wani mai sayar da tayoyi da batur na mota ya rataye kanshi har ya mutu saboda tsananin kuncin rayuwa a Kano.


Kazalika mun kawo maku yadda wani mutum ya banka wa kanshi wuta har ya mutu a jihar Benue saboda tsananin talauci da kuncin rayuwa.

A watanni biyu da suka gabata, mun kawo maku labarin yadda wani matashi ya kashe kanshi a jihar Ebonyi, kazalika haka wani magidanci ya kashe kanshi a jihar Anambra da sauran ire iren wadannan da dama wanda aka alakanta su da dalilin tsananin talauci da kuncin rayuwa.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN