Babban rikici ya barke bayan 'yan daba sun fada kotu tare da fatattakar alkali da lauyoyi


An tsananta tsaro a harabar babbar kotun tarayya da ke Yenagoa, jihar Bayelsa a ranar Juma'a don gudun kutsawar 'yan ta'adda kamar yadda suka yi a ranar Alhamis da rana.

'Yan ta'addan da ke dauke da miyagun makamai, wadanda yawansu ya kai 20, inda suka fi karfin jami'an tsaro kuma suka kutsa cikin kotu mai daraja ta II, wacce take kula da tsayar da 'yan takarar jam'iyyar APC da na PDP a Bayelsa ta tsakiya Sun lalata duk wasu abubuwa masu muhimmanci na ofishin da ake ajiye kayan shari'ar da kuma kayan amfanin kotun, Vanguard ta wallafa.

'Yan ta'addan sun fatattaki lauyoyi da ma'aikatan kotun, sannan sun kwashe kudade, wayoyi da sauran abubuwa masu daraja.A wani labari na daban, shugaban jam'iyyar APC na Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce sai an zage damtse kafin a samu nasarar yaki da 'yan ta'adda a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

A jiya ne Tinubu ya nuna matsananciyar damuwarsa a kan yadda 'yan Boko Haram suka yi wa manoma 43 na jihar Borno kisan wulakanci. Manoman da basu ji ba basu gani ba, sun mayar da hankulansu wurin nema wa iyalansu abinci, amma rashin tsaro ya janyo musu bala'i.

Source: legitLatsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN