Lafiyar al'umma ta ta'allaka ga tsabtataccen abinci- Inji Bright Girls jihar Kebbi


Kungiyar Bright Girls a jihar Kebbi, ta gudanar da ziyarar fadakarwa tare da ilmantarwa gami da bayar da kyautuka ga masu sana'oin sayar da zogale, gumi, nama da sauransu.



Kungiyar karkashin jagorancin shugabanta na jiha Hajiya Luba Sulaiman tare da mukarrabanta sun ziyarci karamar hukumar Birnin kebbi inda shugaban karamar hukumar Birnin kebbi Alh. Aminu S. Fada ya tarbe su. Daga bisani Hajiya Luba ta gabatar da bokitai domin raba wa Yara masu sayar da zogale don ganin cewa ba su yi amfani da hannu kai tsaye ba tare da kariya wajen tu'ammali da sana'ar.



Kazalika kungiyar tare da shugaban karamar hukumar Birnin kebbi ta ziyarci babban kasuwar Birnin kebbi ta zagaya tare da janar Manaja na kasuwar Birnin kebbi Alh. Umar Dangura, da Sakataren kasuwar suka zagaya wajen yan nama, yan zogale da sauran masu sana'ar cimaka, domin ilmantar da su tare da fadakarwa kan yadda za su yi tu'ammali da kudi, jikinsu da kuma sana'a da mutane ke saye, kamar su kuli kuli, wanda ba a dafa shi, su daudawa, kosai cikin kasuwa, kankana da kuma nama. Duk an wayar masu da Kai yadda za su yi tu'ammali tsakanin sana'arsu da kudi.


Kungiyar, ta kuma wayar masu da kai bisa muhimmanci. wanke hannaye da sabulu idan aka yi bahaya ko aka Yi fitsari kàfin a dawo a ci gaba da sana'a.

Tare da shugaban karamar hukumar Birnin kebbi, kungiyar, ta zagaya kasuwar Ambursa, inda suka raba bokitai tare da bayar da horo na yadda za a yi mu'amala da ci maka domin samun ingantaccen lafiya ga al'umma.


A unguwar Takalau a tsohon garin Birnin kebbi, kungiyar ta fadakar wa masu shanya shinkafa a titi su sami tsabtataccen wuri domin yin haka, domin kauce wa yiwuwar dabbibi su hau kan shinkafa da aka baje su yi kashi, fitsari,, wanda idan an gama redawa, kazanta zai iya kasancewa a ciki da zai iya cuta wa jama'a.


Sakataren kungiyar Bright Girls na jihar Kebbi Abubakar Muhammad ABK, ya ce kungiyar za ta ware wasu masu sayar da nama ta basu horo kan yadda za su yi tu'ammali da nama domin mutane su sami gamsuwa wajen sayen sana'arsu.




Yan zogale, dankali da Yan kosai kan hanya, masu sayar da kifi a bude, masu sayar da agashe ba tare da samar da kariya daga kura ko datti ba, kungiyar za ta bayar da horo domin a sami ingantacciyar tsabta a sana'arsu.






Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN