Kwastam sun kama mota maƙare da makamai a Jihar Kebbi


Dakarun hukumar hana fasa ƙwauri na Najeriya Kwastam sun kama wata babbar mota maƙare da bindigogi ƙirar gida a Ƙaramar Hukumar Yauri na Jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin ƙasar.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin Lahadi, inda ta ce bindigogin da aka kama a cikin buhunhuna sun kai guda 73 da kuma harsashi 891.


Mai magana da yawun Kwastam a Najeriya wanda kuma ya sanya wa sanarwar hannu, Joseph Attah, ya ce an kama mutum uku da ke tare da motar kuma tuni an fara bincike a kansu.

Kwamanda mai kula da yankin na Zone B, Hamisu Albashir ya bayyana kamen da cewa "wani saƙo ne ga duk wanda ke yunƙurin shigowa da makamai cikin Najeriya ta Zone B".

Kazalika, ya yi kira ga mazauna yankin musamman na kan iyaka da su kai wa jami'an tsaro da rahoto domin taimaka wa harkar tsaro.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN