GSS Ƙanƙara: Ɓarayin ɗaliban Ƙanƙara sun tuntuɓe mu – Masari


Gwamnatin jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta ce ƴan fashin da suka sace ɗaliban makarantar sakandaren kimiyya ta Ƙanƙara sun tuntuɓi hukuma kuma tuni aka fara tattaunawa kan abin da ya shafi tsaron yara da yadda za a mayar da su gida lafiya.

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Litinin da yamma, bayan da Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya kai wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ziyara garin Daura, kwanaki kaɗan bayan sace ɗaliban a jihar.

A wani saƙon Twitter da shi ma mai taimaka wa shugaban ƙasar kan kafofin sada zumunta, Bashir Ahmed, ya wallafa, ya bayyana cewa Gwamna Masari ya je Daura ne domin ya yi wa shugaban ƙasar ƙarin bayani kan halin da ake ciki dangane da ƙoƙarin da ake yi na gano ɗaliban da aka sace.

Kazalika gwamnan ya sanar da shugaban ƙasar cewa hukumomin tsaro sun gano inda yaran suke a hannun maharan.

Masari ya ƙara da cewa Shugaba Buhari ya damu ƙwarai kan yadda za a ceto ɗaliban, yana mai cewa ya dace ya ziyarci shugaban ƙasar ne kawai don ba shi ƙarin bayani kan halin da ake ciki na ceton.

"Muna samun ci gaba kuma za mu samu nasara,'' kamar yadda gwamnan ya shaida wa ƴan jarida sa'a guda bayan ganawarsa da Shugaba Buhari, wacce ta fara da misalin ƙarfe 2 na rana.

Tun a ranar Juma'a Shugaba Buhari ya tafi mahaifarsa Daura don yin hutu na ƴan kwanaki, sai dai isarsa ke da wuya sai ƴan fashi suka dirarwa makarantar sakandaren ƴan mazan ta Ƙanƙara da ke jihar Katsinan suka sace yara fiye da 300.

Buhari na shan caccaka kan ziyartar shanunsa a Daura

A daidai lokacin da ake tsaka da wannan lamari na alhinin sace ɗaliban Ƙanƙara ne kuma sai kafar yaɗa labaran intanet ta Sahara Reporters ta fitar da wani bidiyo da ke nuna Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci gandun shanunsa da ke garin Daura a ranar Litinin, inda a yanzu haka yake can don shafe kwanaki.

A bidiyon dai an ga Shugaban sanye da takunkumi a fuskarsa, al'amarin da ya sa da yawa suka gaskata bidiyon da cewa sabo ne saboda tun bayan da aka fara kullen annobar cutar korona ba a ga ya je Dauran ba.

Bisa al'ada Shugaba Buhari kan je wajen shanunsa a duk lokacin da ya ziyarci mahaifarsa Daura.

Wannan lamari dai ya jawo masa suka da caccaka daga wajen ƴan Najeriya a Tuwita inda aka ƙirƙiri wani maudu'i mai taken #Cows inda aka yi amfani da shi sau fiye da 14,000 zuwa lokacin wallafa wannan labari.

Da yawan masu amfani da maudu'in suna sukarsa ne da cewa duk da cewa yana cikin jihar Katsinan inda aka sace ɗaliban amma ya gaza zuwa garin da abin ya faru don jajantawa iyayen yaran, sai dai maimakon haka ya tafi gandun shanunsa don duba su.

Yaseer Ismaila kugu ya ce: "Buhari bai damu da komai ba. Ina nufin ana tsaka da kimakin kisan gillar da aka yi wa manoma a Zabarmari da sace ɗaliban makarantar Ƙanƙara ta yaya shugaban wannan ƙasa zai zaɓi ziyartar Daura?"

Abubakar shi ma ya ce: "Buhari yana can yana kula da shanunsa a Daura, amma ya gaza kare rayuka da dukiyoyin mutanensa."

Me jami'an tsaro ke yi don ceto yaran?

A hannu guda ita ma hedikwatar sojin Najeriya ta shaida wa BBC cewa sojoji na bakin kokarinsu wajen ceto yaran.

Manjo-janar John Enanche shi ne daraktan yada labarai na sashen da ke kula da arangamar da sojojin ke yi a sassan Najeriya, ga kuma abin da ya shaida wa Ibrahim Isa a wata hira da suka yi.

Ku latsa lasifikar da ke ƙasa don sauraron hirar

Source: BBCHausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN