Kuma dai: Boko Harm sun sace matafiya 35 a Garin-Kuturu Jakana jihar Borno


Rahotanni daga jihar Borno sun ce yan Boko Haram sun sace mutum 35 matafiya a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri da yammacin ranar Juma'a.

Rahotan TVC NEWS ya ce yan Boko Haram sun farmaki ayarin motocin matafiya ne kusa da garin Garin-Kuturu Jakana da misalin karfe 4 na yamma.

Rahotun ya kara da cewa maharan sun zo ne da motci kirar Hilux guda biyar, sanye da tufafin soji, suka kafa shinge kamar suna duba ababen hawa, daga bisani suka kaddamar da farmakinsu kan matafiya, kuma suka kone wasu motoci kafin su tafi.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN