Jihar Kebbi: Abubuwa 9 da Hisbah ta wajabta da haramta aikata su a Yauri


Hukumar hisbah a garin Yauri da ke jihar Kebbi ta kafa wasu sabbin dokoki ga al’umman jihar a kokarinta na dinke wasu baraka tare da ladabtar da mutanenta.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta kuma wajabtawa limamin da zai daura aure ya tabbatar da an gabatar masa da sakamakon gwaje gwaje da ma’auratan suka yi daga babban asibiti.

Ya kuma haramtawa matasa saka wandon sagin da askin banza.

Jihar Kebbi: Abubuwa 9 da Hisbah ta wajabta da haramta aikata su a Yauri

Jawabin ya zo kamar haka:

“Abubuwan da Hisbah ta hana aikatawa cikin garin Yauri

"1. Gwaji ga Ma’aurata

"Namiji: Gwajin Kanjamau (HIV/AIDS), gwajin Anta (Hypatitis).

"Macce: Gwajin Kanjamau (HIV/AIDS), gwajin anta (Hypatitis), gwajin ciki.

"2. An hana sa wandon sagin

"3. An hana askin banza

"4. An hana P.E.S.

"5. Ba’a kai karfe 6 na marance wajen talla cikin kasuwa

"6. Ba’a daukan mata biyu a mashin sai da lalura

"7. Ba’a awo da kwanon da ya lankwashe

"8. An hana kide-kiden D.J. Da Wasigidi

"9. An hana buga 9jaBet

"Wajibi ne duk Limamin da zai daura Aure ya tabbatar da an gabatar masa da takardar sakamakon gwaje-gwajen da aka yi daga babban likita na babbar asibiti (General Hospital) kafin a daura aure.

"Wanda duk aka samu ya sabama wannan dokan sa’a gabatar dashi gaban shari’a.

"Daga karshe muna rokon Allah ya karemu da miyagun kaddarori."

A wani labarin, Shahararriyar jarumar nan ta Kannywood, Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da Gabon ta yi wa wani dattijo da ya nuna yana kaunarta sha tara ta arziki.

Jarumar ta yi wa dattijon wanda ba a bayyana sunansa ba kyautar kudi har naira dubu dari biyu.

Hakan ya faranta ran tsohon har ya bayyana cewa ya janye tare da yi mata fatan alkhari da tarin addu’o’i.

on sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN