Shakka babu Najeriya za ta tarwatse face an dau mataki- Cewar jigo a Arewa


Farfesa Yusuf Turaki ya ja kunne inda yace akwai yuwuwar Najeriya ta tarwatse a kowanne lokaci daga yanzu matukar aka cigaba da amfani da kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999.

A wata hira da yayi da jaridar The Sun, farfesan ya kwatanta kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999 da abinda ba zai kai kasar nan inda ake tsammani ba.

Turaki ya ce babu shakka kundin tsarin mulkin kasar nan yana daga cikin dalilan da suka hana kasar nan cigaba duk da shekaru 60 da tayi da samun 'yancin kai.

Ya ce: "Abinda na gane shine abinda ke faruwa yanzu yana da tushe da babban tarihi wanda aka gina mana tuntuni. Ina tuna tarihin baya, yadda turawan mulkin mallaka suka kafa kasar nan da muke kira da Najeriya.

"A arewacin Najeriya, na yanke shawarar duba bangarori biyu,, na Musulmi da kuma wadanda ba musulmi ba kuma na so duba yadda turawan mulkin mallaka suka gina dokokinsu."

Turaki ya kwatanta kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999 da damfara a bayyane, kari da cewa duk wanda yace kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999 abun alheri ne ga Najeriya toh son kan shi kawai yake.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN