Hadimin Ganduje ya nemi gafar Kwankwaso sakamakon yi masa karya


Mai ba Gwamnan jihar Kano shawara kan harkokin addini Ali Muhammed Alibaba ya nemi gafarar tsohon Gwamnan jihar Kano Engr Rabiu Musa Kwankwaso.

DailyNigerian ta ruwaito cewa Alibaba ya fada tsaka mai wuya ne bayan yan sandan jihar Kano sun kama shi tare da yi masa tambayoyi bayan Manajan Kampanin man Aliko Oil a Company Ltd  ya shigar da kararsa wajen yan sanda a Bompai ranar Alhamis.

Alibaba ya yi zargi a wani shirin radio cewa Kampanin  man mallakan Kwankwaso ne. Ya kuma kalubalanci Kwankwaso cewa ya rantse idan Kampanin man ba nashi bane.

Ya Kara da cewa kalar fari da ja na Kampanin man ya yi kama da kalar da Kwankwaso ke amfani da shi a siyasarsa.

Bayan yan sanda sun yi masa tambayoyi na tsawon awanni. An yi zargin cewa yansanda sun garkame shi, daga bisani suka bayar da shi beli, da yarjejeniyar cewa zai koma gidan rediyo da ya yi wannan zargi domin ya janye ikirarinsa.

Ranar Asabar Alibaba ya bayyana a shirin gidan rediyo kuma ya janye ikirarinsa tare da ban hakuri ga Kampanin mai na Aliko, da kuma Rabiu Musa Kwankwaso.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN