Alh. Màlami Shekare |
Kungiyar Arewa Publishers Forum of Nigeria (NGO's) ta karrama Sàkataren Din din din na ma'aikatan filaye da gidaje na jihar Kebbi Alhaji Màlami Shekare bisa kokarinsa na samar da ingantaccen tsarin wanzar da muhalli a jihar Kebbi.
Kungiyar ta gabatar da takardar shaidan yabo da karramawa wanda shugaban kungiyar na kasa ya sa wa hannu, a gabatarwa na 2019/2020.
Kafin nadinsa a matsayin Sakataren Din din din na ma'aikatan filaye da gidaje, Alh. Màlami Shekare ya zama Janar Manaja na hukumar bunkasa birane na jihar Kebbi, watau Kebbi Urban Development Authority (KUDA) inda ya sami kyakkyawar yabo daga jama'a da ma'aikatan KUDA bayan ya bar ma'aikatan.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari