Da duminsa: Ganduje ya bada umurnin rufe jami'ar Bayero da manyan makarantu a Kano


Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ta bada umurnin rufe jami'ar Bayero da sauran makarantun gaba da sakandaren dake jihar ba tare da bata lokaci ba, rahoton Daily Trust.

Wannan sanarwan ya zo kwana daya bayan gwamnatin jihar ta kulle dukkan makarantun firamare da sakandaren dake jihar.

A jawabin da kwamishanar ilmin makarantun gaba da sakandare, Dakta Mariya Bunkure, ta rattafa hannu, an umurci dukkan dalibai su koma gidajensu.

"Muna shawartan dukkan dalibai su fita daga cikin makarantu daga ranar 16/12/2020," tace.

Gwamnatin jihar ta yi kira ga daliban su cigaba da bibiyan karatuttukansu yayinda suke zaune a gida.

A jiya mun kawo muku cewa gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu da ke fadin Jihar.

Gwamnatin jihar Kano ba ta bayyana dalilin rufe makarantun ba a cikin gajeriyar sanarwar da kwamishinan ilimi, Sanusi Kiru, ya fitar, kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.

"Mai girma gwamna ya bayar da umarnin gaggauta rufe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu ba tare da bata lokaci ba."

"Ana umartar iyayen da ke da yara a makarantun kwana su je domin dauko 'ya'yansu zuwa gida daga gobe, Laraba, 16 ga watan Disamba, 2020.

"Gwamnati ta na bayar da hakuri a bisa dukkan wani rashin jin dadi da daukan wannan mataki ya haifar," kwamishinan ya fitar.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN