Wani dansanda da ya bugu bayan ya yi tatil da barasa ya saci motar yan sanda a kasar Afrika ta kudu.
Yan sanda na zargin dansandan da aikata ba daidai ba ta hanyar shan barasa yayin da yake tuki tare da yin tatil da barasa. Kazalika ana tuhumarsa da sace motar yansanda tare da tuka ta ba tare da izini ba.
Bayanai sun ce wani faifen bidiyo da ya bayyana a intanet, ya nuna yadda wannan dan sanda ya maka motar a gidan wani. Kuma ya kasa fitowa cikin sauki daga cikin motar.
Ganau ba jiyau ba ya ce dan sandan ya kasa tsayuwa bisa kafafunsa kamar yadda ya kamata domin tsananin buguwa da barasa bayan ya fito daga cikin motar.
An kira yansanda wanda suka kama shi suka yi awon gaba da shi domin bincike..
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari