An kama karuwa da ta sayar da jaririyarta mai wata 4 a kan N300,000 a birnin Katsina (Hotuna)


Rundunar yan sandan jihar Katsina sun kama wata mata mai shekara 25  wacce ke sana'ar zaman kanta mai suna Zainab Adamu bisa zargoin sayar da jaririn da ta haifa akan kudi Naira dubu dari uku N300, 000. .

Mai magana da yawun hukumar yansandan jihar Katsina Isah Gambo ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ranar Laraba 2 ga watab Disamba a Katsina.


Ya ce wacce aka kama yar asalin jihar Adamawa ce, amma tana zauune a unguwaar Kofar Kaura a jihar Katsina

Ya ce " Zainaaba ta hada baki da kawarta Ruth Kenneth mai shekara 32 da ke zaune a unguwar Kofar Kaura, amma yar asalin jihar Delta suka sayar da Jaririyar mai wata hudu ma wani mutum mai suna Chiwendi Omeh mai shekar 43, wanda aya fito daga karamar hukumar Ekwusigo a jihar Anambra a kan N300,000".


Ya ce "Yayin da ake ci gaba da bincike, an sake kama dan uwan Chinwendu mai suna Chukwudi Elias Nnali mai shekara 45 domin taimakawa dumu dumu wajen ganin an tafiyar da harkallar sayar da jaririyar".


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN