Bayan kama shugaban Pension Reform Task Team (PRTT), Abdulrashid Abdullahi Maina ranar 30 ga watan Nuwamba 2020 a Jamhuriyar Niger. Hukumar yansandan Najeriya tana shirye shiryen maido shi Najeriya domin ci gaba da fuskantar shari'a da ke gabansa a Kotu.
Tun farko wata Kotu a Abuja Najeriya ta bayar da umaurnin kama Maina a duk inda aka ganshi a Duniya bayan ya ketare beli. Lamari da ya sa mahukuntan yan sandan Najeriya suka nemi taimakon yansandan kasa da kasa ta INTERPOL domin kama Maina tare da taimakon hukumomin yansanda a Jamhuriyar Niger.
Mai magana da yawun hukumar yan sandan Najeriya Frank Mba, ya sanar cewa Abdulrashid Maina na tsare a Niger yayin da yan sandan Najeriya, INTERPOL da yan sandan Jamhuriyar Niger ke kokarin cika ka'idodi a hukumance domin maido Maina Najeriya.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari