2023: Jami’an gwamnatin Ebonyi sun bukaci Umahi yayi takarar Shugaban kasa


An matsawa gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi lamba a kan ya fito takarar kujerar Shugaban kasa a 2023.

Mataimakin gwamnan jihar, Kelechi Igwe da sauran mambobin majalisar dokokin jihar sun bukaci Umahi da ya kaddamar da kudirinsa na takarar shugaban kasa.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa jami’an sun ziyarci gwamnan a mahaifarsa da ke Uburu, karamar hukumar Ohaozara don tattauna lamarin tare da shi.

Da yake magana a madadin sauran jami’an, mataimakin gwamnan ya ce sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) saboda Umahi.

Ya ce:

“A sanda ka sanar cewar lokaci yayi da za a tafi gaba, da yawa daga cikinmu muna ta jan kafa, muna ta son tattaunawa amma a karshe, sai muka yanke shawarar tafiya da kai. Dole in fada maka gaskiya cewa wasunmu basu so APC ba amma muka yanke shawarar komawa saboda kai. Don haka, muna kaddamar da cewa dole ka tsaya takarar kujerar Shugaban kasa.”

Gwamnan, a martaninsa ya bukaci jami’an da su ci gaba da ba APC goyon baya. Ya ce jam’iyyar ta samar da wata kafa ga yan Igbo domin su kimanta kansu da kyau.

Sai dai Umahi bai bayyana ko zai yi takarar Shugaban kasa a zaben 2023 ba.

A wani labarin, majalisar Kansiloli ta tsige Shugaban Ƙaramar Hukumar Shiroro, Kwamred Dauda Suleiman Chukuba, bisa zargin Almundahana.

A cewar majalisar, sun bawa shugaban duk wata dama domin ya kawar kansa daga zargin da ake yi masa amma sai ya nuna musu raini.

Ana zargin Kwamred Chukuba da yin almubazzaranci da barnatar da kudaden shiga da karamar hukuma ta samu.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN