Zaben Amurka: Dan takaran Democrat ya sami kuri'a da ba a taba samu ba a tarihin zaben Amurka


Tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka kuma dan takaran jam'iyar Democrat a zabem shugaban kasar Amurka Joe Biden ya kafa tarihi kasancewa mutumin da ya fi kowane dan takaran shugaban kasar Amurka yawan kuri'u a tarihin zaben shugaban kasar ta Amurka.

Ya zarce yawan kuri'u da tsohon shugaba Barak Obama ya samu a zaben 2008 da karfe 8 na safe agogon Amurka ranar Laraba 4 ga watan Nuwamba.

Duk da ba a kidaya kuri'un sauran jihohi ba, Joe Biden yana da kuri'u 69,629,972, a cewar Associated Press..


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Previous Post Next Post
Latsa nan ka shiga group din mu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN